Ya kamata a rage yawan kulob din gasar Premier

rosell Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sandro Rosell

Shugaban Barcelona Sandro Rosell ya ce akwai bukatar rage yawan kulob din dake taka leda a gasar premier don taimakawa gasar Zakarun Turai.

Rosell wanda shine mataimakin shugaban kungiyar masu kulob a Turai wato ECA, ya ce yanason a buga wasu wasannin Turai a karshen mako sannan a rage buga wasannin sada zumunci.

Yace"ya kamata mu shawokan gasar premier ya koma 16, ta yadda wata rana Barcelona zata fafata da Manchester United a ranar Asabar".

A cewarsa, manufar rage yawan kulob daga 16 zuwa 20 don a baiwa 'yan wasa hutu ne.

Rosell yace ba za a cimma burin da aka sa a gaba ba, idan har gasa a Ingila da Spain da kuma Italiya suna da kulob ashirin.

A jawabinsa a wani taro a Doha na Qatar, Rosell ya gargadi Uefa cewar kungiyar ECA ba zata sabunta yarjejeniyar dake tsakaninsu ba idan ya kare a shekara ta 2014.