BBC ta kebe sunaye biyar don bada kyauta

afouy Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zaratan 'yan kwallon Afrika

Latsa nan don kada kuriarka

BBC ta bayyana sunayen 'yan kwallo biyar wanda za a baiwa daya daga ciki gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a shekara ta 2011.

'Yan wasa sune 'yan kasar Ivory Coast Yaya Toure da Gervinho da dan Ghana Andre 'Dede' Ayew sai Samuel Eto'o na Kamaru da kuma Seydou Keita na Mali.

Masoya kwallon kafa ne zasu kada kuri'a kafin a rufe zaben a ranar tara ga watan Disamba.

Za a sanarda sunan wanda ya lashe kyautar a ranar 16 ga watan Disamba a shirin BBC Sport Today.

Dan Manchester City Yaya Toure da na Arsenal Gervinho sun bugawa Ivory Coast kwallo a wasanni share fagen neman gurbin zuwa gasar kwallon kasashen Afrika da za ayi a 2012 inda kasar ta lashe duka wasanninta.

Toure ne yaci kwallon daya baiwa Manchester City kofin gasar FA ta Ingila a yayinda shi kuma Gervinho ya taimakawa Lille ta lashe kofina biyu a gasar kwallon Faransa kafin ya koma Arsenal.

Sunayen wadanda aka kebe:

* Andre Dede Ayew * Samuel Eto'o * Gervinho * Seydou Keita * Yaya Toure

Ayew na daga cikin 'yan wasan Ghana da suka taimakawa Marseille ta lashe kofin kwallon Faransa da kuma na Super Cup a yayinda dan Mali Seydou Keita yana cikin tawagar Barcelona data lashe gasar kofin zakarun Turai.

Eto'o ya zira kwallaye 21 a gasar kwallon Italiya lokacin yana murza leda a Inter Milan kafin ya koma kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha a watan Agusta.

Wasu kwararru ne a fannin kwallon Afrika ne suka zauna suka tantance wadanda suka fi dacewa da samun kyautar.

Wadanda suka taba samun kyuatar gwarzon dan kwallon Afrika na BBC

2010 - Asamoah Gyan (Sunderland & Ghana)

2009 - Didier Drogba (Chelsea & Ivory Coast)

2008 - Mohamed Aboutrika (Al Ahly & Egypt)

2007 - Emmanuel Adebayor (Arsenal & Togo)

2006 - Michael Essien (Chelsea & Ghana)

2005 - Mohamed Barakat (Al Ahly & Egypt)

2004 - Jay Jay Okocha (Bolton & Nigeria)

2003 - Jay Jay Okocha (Bolton & Nigeria)

2002 - El Hadji Diouf (Liverpool & Senegal)

2001 - Sammy Kuffour (Bayern Munich & Ghana)

2000 - Patrick Mboma (Parma & Cameroon)