Tarihin kwallon Samuel Eto'o na Kamaru

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o Fils na Kamaru

Sauya sheka daga zakarun kwallon Italiya wato Inter Milan zuwa gasar kwallon Rasha, abune da za a iya cewa saboda batun kudi ne Eto'o ya tafi.

A yanzu dai shine dan kwallon da yafi kowanne karbar albashi a duniya inda ya kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da Anzhi Makachkala a yayinda rahotanni ke nuna cewar yana samun fan dubu dari uku a kowanne mako.

Amma kuma Eto'o ya ce bawai batun kudi ne kawai ya sashi sauya sheka ba. Anzhi dai a yanzu tana haskakawa a gasar kwallon Rasha saboda mai kulob din ya kashe makudan kudade.

Suleiman Kerimov attajirai mai kasuwancin a fannin man fetur shine kuma mai kulob din kuma arzikinsa ya kai dala biliyon 7.8.

'Yan wasan Anzhi na zaune ne a wani sansani dake wajen birnin Moscow kuma a nan suke horo saboda dalilan tsaro. Amma suna tafiya garin Makhachkala a duk lokacin da zasu buga wasansu na gida.

Duk da irin rashin tsaro dake Dagestan saboda masu fafutuka na Islama, Anzhi ta iya siyo Roberto Carlos da kuma Yuri Zhirkov.

Eto'o ya bayyana komawarsa Anzhi a matsayin "wani mafarki kuma abun mamaki".

Dan wasan dai yanada farin jini tsakanin magoya bayan Anzhi saboda yaci kwallo a wasansa na farko a kulob din a watan Agusta sannan kuma ya cigaba da haskakawa.

Eto'o ya ce yanasaran lashe kofin gasar kwallon Rasha don ya buga gasar zakarun Turai tare da Anzhi.

Eto'o a baya ya murza leda a Barcelona da Mallorca da kuma Real Madrid.

Ya kuma kasance dan kwallon Afrika da yafi kowanne samu kyuata saboda ya lashe kyuatar gwarzon dan kwallon Afrika na CAF sau hudu sannan ya lashe kofin zakarun Turai sau uku.

Ya lashe gasar kwallon Spain data Italiya da kuma na kofin kwallon kasashen Afrika sau biyu tare da Kamaru da kuma zinare a gasar Olympics.

Bayan lashe kofin zakarun Turai da Barcelona a 2006 da kuma 2009, dan wasan Kamarun din ya lashe gasar tare da Inter Milan a shekara ta 2010.

Eto'o bai taba lashe kyautar gwarzon dan Afrika na BBC ba.