Fecafoot ta gayyaci Eto'o akan batun da'a

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Kamaru wato Fecafoot ta gayyaci Samuel Eto'o da Eyong Enoh su gurfana gaban kwamitin da'a don kare kansu akan batun yajin aikin da 'yan kwallo suka yi a makon daya gabata.

Rashin jituwa akan batun kudin alawus ya janyo an fasa buga wasan sada zumunci tsakanin Kamaru da Algeria.

Ana saran su biyun zasu kare kansu a gaban kwamitin a ranar Alhamis, amma watakila su nemi a dage ranar idan har aka bukaci ganinsu a zahiri.

Har wa yau kuma 'yan wasan na bukatar bayyanar jami'an Fecafoot dake cikin takaddamar.

Takaddamar ta taso ne bayanda 'yan wasan Kamaru suka buga wasanni biyu tare da Morocco da Sudan a birnin Marrakesh, amma kuma sai aka ki biyansu kudin alawus dinsu.

Shi kuma dan kwallon Tottenham Hotspur Benoit Assou-Ekotto an nemi ya kare kansa akan kin amsa gayyatar buga wasan a Morocco.

Eto'o da Assou-Ekotto a tsakiyar wannan shekarar sun taba bayyana gaban fecafoot akan batun rashin da'a.

Karin bayani