Abramovich baya kokwanto akai na-Villas-Boas

villas-boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Villas-Boas na fuskantar matsin lamba

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya hikakance cewar mai kulob din Roman Abramovich baya kokwanto akansa bayan da aka doke kulob din a wasanni uku cikin hudu na gasar Premier ta Ingila.

Tun a ranar Lahadi, Chelsea ta bayyana rahotannin takun saka tsakanin su biyun a matsayin labari mare tushe.

Bayan Chelsea ta sha kashi a wajen Liverpool daci biyu da daya, Villas-Boas ya ce baida shakka mai kulob din na goyon bayansa.

Villas-Boas yace"batu ne yin hakuri, kamar yadda na fada mun shirya gina wani sabon abu a kulob din kuma mun shirya samarwa kulob din makoma me kyau".

Wannan rashin nasarar da Chelsea ta yi, ya nuna cewar Manchester City na gaban Chelsea da maki 12, abinda yasa Villas-Boas ya amince akan cewar suna fuskantar babban kalubale wajen kokarin lashe gasar Ingila.

Masu horadda wasan da suka yi aiki a karkashen Roman Abramovich:

* Claudio Ranieri, Yuli 2003*-Mayu 2004 * Jose Mourinho, Yuni 2004-Satumba 2007 * Avram Grant, Satumba 2007-Mayu 2008 * Luiz Felipe Scolari, Yuli 2008-Fabarairu 2009 * Guus Hiddink, Fabarairu-Mayu 2009 * Carlo Ancelotti, Yuni 2009-Mayu 2011 * Andre Villas-Boas, Yuni 2011- har yanzu

*Abramovich ya sayi kulob din a watan Yulin 2003.

Karin bayani