Bin Hammam ya daukaka kara zuwa CAS

Mohammed Bin Hammam Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammed Bin Hammam

Korarren shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya, Mohammed Bin Hammam ya daukaka kara akan dakatar dashi na tsawon rai da Fifa tayi masa, kamar yadda kotun sauraron kararrakin wasanni CAS ta bayyana.

Sanarwar da CAS ta fitar ta ce" Hammam na bukatar a soki hukuncin Fifa akansa".

Dan kasar Qatar din a watan Yuli ne aka same shi da laifin kokarin bada dala dubu 40 ga jami'an kwallon yankin Caribbean don sayen kuri'arsu a zaben shugaban Fifa.

Bin Hammam ya rasa mukaminsa ne a matsayin shugaban kwallon nahiyar Asiya sakamakon hukuncin Fifa inda dan China Zhang Jilong ya maye gurbinsa.

Bin Hamman dai ya sha alwashin wanke sunansa, inda ya bayyana tuhumar da ake yi a matsayin batu na siyasa.

Dakatar dashi ya tilastashi janyewa daga zaben shugabancin Fifa, abinda ya baiwa Sepp Blatter damar cin zabe a karo na hudu.

Karin bayani