FIFA: Ivory Coast ce ta farko a Afrika

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaya Toure na Ivory Coast tare wasu 'yan Afrika ta Kudu

Ivory Coast ce ta farko a fagen kwallon kafa a nahiyar Afrika kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fidda jerin karfin kasashe.

Sai dai Ivory Coast din ce ta goma sha shida a duniya, a yayinda Ghana take ta biyu a Afrika amma kuma ta 29 a duniya.

Algeria ce ta uku a Afrika sai Masar ta Hudu a yayinda Najeriya ke ta biyar a Afrika amma ita ce ta 43 a duniya.

Sauran kasashen da suke goma na farko a Afrika sune Kamaru, Afrika ta Kudu Cape Verde da kuma Ghana.

Har yanzu dai Spain ce ta farko a duniya a yayinda Netherlands ke ta biyu sai kuma Jamus ke matakin na uku.

Jerin goma na farko a duniya:

1. Spain 2. Netherlands 3. Jamus 4. Uruguay 5. Ingila 6. Brazil 7. Portugal 8. Croatia 9. Italiya 10. Argentina

Karin bayani