Anderson ba zai taka leda ba na wata uku

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan, Manchester United, Anderson

Dan wasan tsakiyan Manchester United, Anderson ba zai taka leda ba daga yanzu har sai watan Fabrairun badi saboda zai yi jinyar raunin da ya samu a gwiwarsa.

Kocin kungiyar Sir Alex Ferguson ne ya bada tabbacin hakan.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 23, ya garzaya Portrugal domin ganawa da wani likita na musamman wanda zai yi mishi tiyata.

Anderson dai bai taka leda ba, tun a wasan da kungiyar ta buga da Otelul Galati a ranar 2 ga watan Nuwamba a gasar zakarun Turai, saboda raunin da ya samu.

Ferguson ya ce baji dadin labarin ba.

Ganin cewa Tom Cleverley shima yana fama da rauni, rashin Anderson zai zama babban kalubale ga United, a kokarinta na kamo City wadda ke jan ragama a gasar ta Premier.