Ferguson na kokwanto kan amfani da na'ura

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin, Manchester United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce yana da shakku a kan fara amfani da na'urar dake tabbatar da kwallo ta shiga raga a gasar Premier a badi.

Hukumar FA dai a wannan makon ta ce za ta duba yiwuwar amfani da fasahar a kakar wasanni ta shekara ta 2012-13.

Ferguson ya ce: "Shawara ce mai kyau, amma bana zatan za'a iya fara amfani da shi daga badi."

Kocin Arsenal, Arsene Wenger shima yana goyon bayan amfani da na'urar kuma ya yi kiran da ayi gaggawar tabbatar da hakan.