U23:Morocco ta doke Najeriya daci daya

Pim Verbeek Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin tawagar Morocco Pim Verbeek

Morocco ta samo gasar kwallon Afrika ta 'yan kasada shekaru 23 da kafar dama bayan ta samu galaba akan Najeriya daci daya me ban haushi a wasan da suka buga ranar Asabar a Tangiers.

Abdelaziz Barrada ne ya ciwa Moroccon kwallonta a bugun fenariti.

Alkalin wasa ya baiwa Morocco fenariti ne bayan dan Najeriya Emmanuel Anyanwu ya kada Yacine Qasmi a kusada gola.

A daya wasan da aka buga a ranar Asabar Algeria ta doke Senegal daci daya me ban haushi.

A ranar Lahadi za a buga wasanni biyu, Masar zata hadu da Gabon sai kuma Afrika ta Kudu ta fafata da Ivory Coast.

Kasashe uku ne zasu tsallake zuwa gasar Olympics a London sai kuma kasa ta hudu ta hadu da wata kasar yankin nahiyar Asiya.

Karin bayani