'Yan kwallo na juyayin mutuwar Gary Speed

speed Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Juyayin mutuwar Gary Speed

'Yan wasan kwallon kafa na cigaba da nuna juyayi a bisa mutuwar kocin kasar Wales, Gary Speed wanda ya mutu a ranar Lahadi yanada shekaru arba'in da biyu.

Kocin West Ham Sam Allardyce ya bayyana mutuwar a matsayin abun takaici saboda Speed gogaggen dan kwallo ne.

Tsohon dan wasan Leeds Gordon Strachan ya ce Gary Speed "mutumin jama'a ne kuma akwai matukar wuya a gane dalilan da suka sanya shi daukar wannan matakin".

David Beckham kuwa ya bayyana Speed a matsayin kwararren dan kwallo wanda ya mutu a lokacin da ake bukatar kwarewarsa wajen horadda 'yan kwallo.

Speed ya zama mai horadda 'yan kwallon Wales ne a watan Disambar 2010 kuma a farko wannan watan tawagarsa ta haskaka fiye da yadda aka zata.

Nasara daci hudu da daya a wasan sada zumunci tsakaninsu da Norway, itace nasara ta uku a jere da Speed ya jagoranci Wales.

Speed ya bugawa kasarsa Wales kwallo a wasanni 85 cikin shekaru 14.