U 23: Dole ne sai Najeriya ta zage damtse

Austin Eguavon Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin 'yan kasada shekaru 23 Austin Eguavon

Dole ne sai tawagar Najeriya ta 'yan kasada shekaru 23 ta zage damtse inda har tanason tsallakewa zuwa wasan kwallon kafa na Olympics, kamar yadda wani dan wasa Danny Uchechi ya bayyana.

An doke tawagar Najeriya ne a wasan farko tsakaninta da Morocco daci daya me ban haushi.

Najeriya zata hadu da Senegal a wasanta na biyu a ranar Talata.

Uchechi yace"Muna bukatar muyi aiki tare a matsayin tawaga don samun nasara".

Ya kara da cewar "kamata yayi muyi wasa fiye da haka, kuma mun gano kura-kuranmu".

Najeriya ce ta lashe gasar kwallo a Olympics a shekarar 1996 sannan ta samu kyautar azurfa a shekaru hudun da suka wuce.

Karin bayani