Namibia za ta daukaka kara a kan Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Herve Zengue, dan wasan da ake cece kuce a kan sa

Hukumar kwallon Namibia za ta garzaya kotun daukaka karar wasanni, domin ta maye gurbin Burkina Faso a gasar cin kofin Afrika ta 2012.

Namibia dai na son a fidda Burkina Faso a cikin jerin kasashen da za su taka leda a gasar saboda ta yi amfani da dan wasan da bai cancanta ba a wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika.

Namibia dai ta kai kukanta a gaban Hukumar kwallon Afrika, wato Caf, amma hukumar ta yi fatali da kukan a makon da ya gabata.

"Mun amince cewa lauyoyin mu su daukaka kara." In ji Barry Rukoro, Sakataren Janar din Hukumar kwallon Namibia.

Takkadamar dai ta kunno kai ne bayan da Burkina Fado ta yi amfani da Herve Zengen a wasanni biyu, wanda kuma aka haifa a Kamaru.

Namibia dai ta ce Zengue bai cika sharudan Fifa ba, kafin ya takawa Burkina Faso.