Zamu taka rawar gani a Disamba- Villas Boas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce kungiyar za ta zage damtse a watan Disamba, bayan kashin da ta sha a hannun Liverpool, a wasan gab da kusa dana karshe a gasar kofin Carling.

Chelsea wadda itace ta biyar a tebur za ta kara da Newcatsle wadda itace ta hudu a karshen makon a gasar Premier.

Sannan kuma bayan wasanni biyu ta hadu da Manchester City.

Har wa yau, Chelsea za ta hadu da Valencia a gasar zakarun Turai a ranar talata mai zuwa a kokarinta na tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar.

"Idan har muna so mu lashe gasar Premier, dolene mu zage damtse a watan Disamba," In ji Kocin Chelsea.

Kocin dai bai yi korafi game da kashin da kungiyar ta sha a hannun Liverpool ba a filin Stamford Bridge, ya dai amince cewa dolene kungiyar ta kara himma.

An dai doke Chelsea a wasanni hudu a gasar Premier, kuma a cikin wasanni tara da kungiyar ta buga a jere ta sha kashi a wasanni biyar.