Courbis ne mai baiwa tawagar Nijar sahawara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roland Courbis, mai baiwa tawagar kwallon Nijar shawara

Dan faransa Rolland Courbis ya zama mai baiwa, tawagar kwallon Nijar shawara a gasar cin kofin Afrika da za'a shirya a badi.

An dai daure Rolland Courbis wanda tsohon kocin Marseille ne a gidan kaso na wani dan lokaci saboda wata badakalar musayar 'yan wasa.

Hukumar kwallon Nijar dai ta ce ta dauki tsohon kocin aiki ne, domin ya sa ido a gasar cin kofin Afrika da za ta halarta a karo na farko a badi.

"Zai zama mai baiwa kocin mu Harouna Douala shawarwari". In ji Djibrilla Hamidou Shugaban Hukumar kwallon Nijar.

Kocin dai na tare da tawagar Nijar din a wasanni sada zumunci da ta buga a Dubia da kuma Botswana a 'yan makwannin da su ka gabata.