A fidda Chinedu Obasi daga tawagar Hoffenheim

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Najeriya, Chinedu Obasi, na taka leda a kungiyar Hoffenhiem

An fidda sunan dan wasan Najeriya, Chinedu Obasi daga tawagar kungiyarsa ta Hoffenhiem a Jamus saboda ya makara zuwa horo.

An dai cire dan wasan ne tare da abokin wasansa dan kasar Brazil, Firmo saboda shim ya aikata lafin m akaran zuwa horo.

Shugaban kungiyar Ernst Tanner, ya ce duk da cewa ana biyan 'yan wasan makudan kudade basa zuwa aiki cikin lokaci.

Firmino dai ya zura kwallo a wasan da kungiyar ta buga daya da daya da Freiburg a ranar asabar din da ta gabata.

'Yan wasan dai ba za su taka leda ba a wasan da kungiyar za ta buga da Bayer Leverkusen a karshen mako.

Tanner ya ce shi da kocin kungiyar Holger Stanislawski sun amince da daukar matakin, saboda 'yan wasan sun saba zuwa horo a makare.