Olympic 2012 za ta lashe kudi fiye da kima

Dandalin wasanni na Olympic Park a London
Image caption Dandalin wasanni na Olympic Park a London

Ofishin mai Binciken Kudi na Kasa a Burtaniya ya yi gargadin cewa idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba, gasar Olympic ta 2012 za ta lashe fiye da kudin da aka kasafta, wato fam miliyan dubu tara da dari uku.

Ranar Litinin gwamnatin kasar ta Burtaniya ta ce za a bukaci karin fam miliyan dari biyu da saba'in da daya don biyan masu gadi, al'amarin da ya sa Ofishin ya ce akwai kasadar kudin da za a kashe a kan samar da tsaro ya rubanya.

Ministar 'yan adawa mai kula da Olympics, Tessa Jowell, ta ce: "Ai da ma wannan harka ce mai cike da kasada".

Ministocin gwamnati dai sun nace cewa akwai fam miliyan dari biyar a wani asusun ko-ta-kwana wanda ba kasafta ba.

Sai dai Ofishin mai Binciken Kudin ya ce Hukumar Shirya Gasar Olympic za ta kammala aikin ginin dandalin wasanni na Olympic Park a kan lokaci kuma ba za ta kashe kudin da ya zarta abin da aka kasafta ba.

Karin bayani