Zan kai Sunderland ga gaci —Martin O'Neill

Martin O'Neill Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon kocin Sunderland, Martin O'Neill

Martin O'Neill ya sha alwashin yin iyaka iyawarsa don kai Sunderland, kulob din da ya goyawa baya yana yaro, ga nasara.

O'Neill, mai shekaru 59 da haihuwa, ya sa hannu a kan wata yarjejeniya wadda za ta ba shi damar maye gurbin Steve Bruce; a gabansa kuma kulob din ya sha kashi a hannun Wolves ranar Lahadi.

Kwallaye biyun dan wasan gaba na Wolves, Steven Fletcher, ya zira a ragar Sunderland sun ba O'Neill damar ganin irin kudar da kulob din ke dandanawa a kakar wasanni ta bana: hasali ma dalilin da ya sa aka gayyato shi ke nan ya baro gudun hijirar da ya ke yi na watanni goma sha bakwai tun bayan barinsa Aston Villa.

"Zan yi iya bakin kokarina don ganin mun samu nasara a wannan lokaci; abin ma da ya kawo ni ke nan", in ji O'Neill.

Sunderland dai sun yi fatan samun nasara a karo na farko a wasanni biyar, amma kuma suka barar da wata dama da kuma bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida.

Yau Litinin O'Neill, wanda ya kalli wasan a cikin 'yan kallo, zai karbi ragamar kulob din, kuma zai kasance a bencinsu ranar Lahadi a wasan Premier da su buga da Blackburn.

Da maki daya Sunderland ta ketare layin masu fadowa a tebur, kasasncewar wasanni biyu kacal ta ci a kakar bana.