Za a fafata tsakanin Manchester City da United

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Manchester United

Manyan abokan hamayya, watau Manchester City da Manchester United za su kara da juna a zagaye na uku na gasar FA.

United ce dai za ta je filin wasa na Etihad, inda za ta so rama cin da Manchester City ta yi mata a wasan da suka yi, wanda suka ta shi City na da shida, ita kuma United na da ci daya.

Kulob din Arsenal zai kara da Leeds, Aston Villa kuma za ta bakwanci Bristol Rovers, Tottenham za ta kara da Cheltenham Town.

Kulob din Tamworth ma zai kara da Everton, Wrexham kuma ya buga da Brighton, sannan Fleetwood zai kara da Blackpool , idan ya lashe wasan da za a sake yi tsakaninsu da Yeovil.

Fafatawar da za a yi tsakanin Manchester City da United ita ce za ta kasance fafata wa mafi zafi, kasancewa City ne ke kan gaba, yayin da United ke biye mata a baya a kan teburin Premier League.