Mikel Arteta ya yabawa Van Persie

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mikel Arteta

Dan wasan Arsenal, Mikel Arteta, ya yabawa kaftin din kulob din, Robin van Persie, bayan buga wasan da suka yi ranar Asabar inda suka ci Wigan hudu.

Arteta ya bayyana Van Persie da cewa kwararre ne matuka a fagen kwallon kafa.

Van Persie dai ya zura kwallaye goma sha shida tun zuwan Arteta kulob din a karshen watan Agusta, abin da ya sanya kulob din ya koma mataki na biyar a gasar Premier League.

Arteta dai ya ce Van Persie na burge shi musamman yadda ya ke zura kwallo.

Sai dai ya yi fatan ganin sauran 'yan wasan kulob din za su rage yawan nauyin da Van Persien ke dauka, idan za su buga wasanni a makonnin da ke tafe.