FIFA ta dakatar da wallafa wasu bayanai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sepp Blatter

Shugaban FIFA, Sepp Blatter, ya ce za a dakatar da wallafa wasu takardu da suka shafi zargin karbar cin hancin da ake yiwa wasu manyan jami'an hukumar daga wajen kamfanin tallace-tallace na ISL.

A wani shiri mai suna Panorama da BBC ta gabatar a bara dai, ta yi zargin cewa manyan jami'an hukumar sun karbi cin hanci daga kamfanin ne don ba shi tallace-tallace.

Bayan hakan ne shugaban FIFA ya sha alwashin buga takardun a ranar sha bakwai ga watan Disamba don sanin gaskiyar abin da ya faru.

Sai dai yanzu Mr Blatter ya ce ba za a wallafa takardun ba saboda bangarorin da abin ya shafa sun kai kara a gaban kotu don hana hukumar wallafa takardun.

A cewarsa za a wallafa takardun bayan kammala sauraron karar da mutanen suka shigar.