Ana gudanar da bincike a kan Suarez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luis Suarez

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce tana gudanar da bincike game da daga dan yatsan da dan wasan Liverpool, Luis Suarez, ya yi da zummar tantance abin da ya ke nufi bayan kulob din Fulham ya ci su daya a wasan da suka yi .

Suarez dai ya daga dan yatsansa na tsakiya ne da ke hannun hagu a lokacin da yake ficewa daga filin wasan Craven Cottage ranar Litinin.

Kocin Liverpool, Kenny Dalglish, ya ce bai ga hoton daga dan yatsan da Suarez ya yi ba, yana mai cewa idan har ya tabbata cewa ya daga yatsan, za a dauki mataki game da batun.

Daga dan yatsa na nufin zagi.

Da ma dai Suarez na fuskantar tuhuma daga hukumar kwallon kafa ta Ingila game da zargin nuna wariyar launin fata.