Anelka na shirin komawa China

Image caption Anelka

Dan wasan Chelsea Nicholas Anelka na tattauna wa da kulob din League na China mai suna Shanghai Shenhua don yiwuwar sayensa.

BBC ta fahimci cewa wakilan Anelkan sun gana da na kulob din domin yiwuwar komawarsa cikin makonni uku masu zuwa.

Babu cikakken bayani game da farashin da aka sanya akan dan wasan.

Chelsea ta sayi Anelka a shekarar 2008 akan fan miliyan sha biyar, inda ya zura kwallaye hamsin da tara a wasanni dari da tamanin da biyar da ya bugawa kulob din.