' Villa zai zama dan dumama-kujera idan…'

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption David Villa

Tsohon jami’in Real Madrid, Jorge Valdano, ya ce dan wasan Barcelona, David Villa, zai kasance dan dumama-kujera idan ba a saka shi a wasan da za su yi da Real Madrid ba.

Villa dai ya buga wasa mai kayatarwa a Camp Nou lokacin kakar wasan bara bayan ya bar Valencia zuwa Real Madrid a watan Mayu na shekarar 2010.

Sai dai yanzu yana kokawar shiga cikin ‘yan wasa goma sha dayan farko na kocin kulob din Guardiola, a kakar wasan bana.

Ganin cewa a kwanan baya ne kulob ya sayi ‘yan wasa kamar Cesc Fabregas da Alexis Sanchez, Villa na fuskantar barazana wajen shiga wasannin da za a yi.

Don haka ne ma, Valdano ya ce idan ba a sanya Villa a gasar wasan el-classico da za a buga ranar Asabar, mai yiwuwa ya kare a zaman benchi.