An rage haramcin wasanni a kan Wayne Rooney

Dan wasan gaba na Ingila, Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Dan wasan gaba na Ingila, Wayne Rooney

An rage haramcin da aka yiwa dan wasan gaba na Ingila, Wayne Rooney, a Gasar cin Kofin Kasashen Turai ta 2012 daga wasanni uku zuwa wasanni biyu bayan ya daukaka kara ga UEFA a Switzerland.

An dai hukunta Rooney ne bayan an sallame shi daga filin wasa saboda ya tokari Miodrag Dzudovic yayin karawarsu da Montenegro a watan Oktoba, lokacin da suka tashi biyu da biyu.

A yanzu dai Rooney, dan shekara ashirin da shida da haihuwa, zai buga wasan Ingila na uku a Rukunin 'D', wasan da za su buga da masu karbar bakuncin gasar, Ukraine; sai dai ba zai buga wasan Ingila da Faransa da kuma na Ingila da Sweden ba.

Za a dage haramcin buga wasa na ukun ne har sai bayan shekaru hudu.

Wani mai magana da yawun UEFA ya shaidawa BBC cewa za a aiwatar da haramcin wasa na ukun ne kawai idan ya aikata mugun hali a wani wasa na daban na Gasar Turai.

Rooney ya kuma amince ya yi aikin raya al'umma na yini daya, a cewar mai magana da yawun UEFA.