Fitar da United babban bala'i ne —Evra

Patrice Evra
Image caption Dan wasan Manchester United, Patrice Evra

Dan wasan baya na Manchester United, Patrice Evra, ya bayyana fitar da kulob din nasa daga Gasar Zakarun Turai da cewa "abin-kunya" ne kuma "babban bala'i".

Kulob din, wandanda suka lashe gasar har sau uku, sun sha kashi ne a Basel da ci biyu da daya, abin da ya sa suka kare a matsayi na uku a Rukunin 'C' kuma za su sauko zuwa Gasar cin Kofin Europa.

A cewar Evra, "abin kunya ne mu yi wasa a gasar Europa; ina bugawa Manchester United kwallo ne don kasancewa a Gasar Zakarun Turai.

"Wannan wani babban bala'i ne. Muna takaici amma kuma mun cancanci fita".

United ne dai kulob na farko da aka yi waje da su a wannan zagayen, hakan ne kuma karo na uku a shekaru goma sha bakwai da aka fitar da su daga gasar zaratan kungiyoyin kwallon kafa na Turai a wannan matakin.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daga hagu: Rio Ferdinand, da Wayne Rooney, da Patrice Evra bayan Manchester United sun sha kashi

Hakan kuma na nufin sun rasa kudin shigar da suka kai fam miliyan ashirin sannan kuma ba za su fito ba a gasar UEFA, inda ake buga akasarin wasanni ranar Alhamis da dare.

United din dai sun kai zagaye na karshe a gasanni uku na baya-bayan nan na zakarun na Turai, inda suka casa Chelsea a shekarar 2007, suka kuma sha kaye a hannun Barcelona a shekarun 2008 da 2010.

"Wannan abin takaici ne", in ji Evra, wanda ya kwashe shekaru shida yana bugawa United wasa; yana ma cikin wadanda suka bugawa kulob din lokacin da suka zo na biyu a gasar a shekarar 2004.