Vidic ba zai buga sauran wasannin bana ba

Nemanja Vidic
Image caption Ana ficewa da Nemanja Vidic bayan ya yi rauni a Basel

Manchester United sun tabbatar da cewa kyaftin dinsu, Nemanja Vidic, ba zai buga sauran wasannin kakar wasanni ta bana ba saboda raunin da ya yi a gwiwa a wasansu na Gasar Zakarun Turai, inda suka sha kaye a Basel da ci biyu da nema.

Dan wasan na tsakiya ya murgude gwiwarsa ta dama ne bayan sun yi karo da Marco Streller na Basel kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kocin United, Sir Alex Ferguson, ya bayyana cewa: "Nemanja ba zai buga sauran wasanni ba; wannan labari ne maras dadi".

Ya kara da cewa "lokacin da na ga raunin na san mummunan rauni ne".

Ferguson dai ya yi fatan kyaftin din nasa ba zai wuce makwanni biyu ba zai ci gaba da wasa, amma hakan ba za ta samu ba. Wannan dai mugun labari ne ga United, wadanda abubuwa suka yi musu kyau a wasanni shida daga cikin takwas tun bayan dawowar Vidic daga wani raunin a watan Oktoba.

Mai yiwuwa a maye gurbinsa da Evans, ko Phil Jones, ko Chris Smalling.

A karawarsu da Wolves a karshen wannan makon dai Ferguson zai shiga fili ne babu zababbun 'yan wasa tara, a wasan da samun nasara zai kai kulob din dab da Manchester City, wadanda ke saman tebur.

Karin bayani