An dakatar da dan kwallon zari-ruga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan kwallon zari-ruga

Hukumar kula da kwallon zari-ruga ta duniya ta ce wani dan wasa da ba ta ambaci sunansa ba ya fadi a gwajin miyagun kwayoyi da ta yi masa

Hukumar ta ce dan wasan yana yi wa wata kasa- da aka boye sunanta, wasa wacce ta gaza zuwa matsayin dab da na kusa da na karshe a gasar da ake yi.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce:'' an dakatar da dan wasan, sai bayan an gama sauraron bahasi a game da batun''.

Hukumar dai ta sanya 'yan wasa 76 sun ba ta jininsu, guda 216 kuma suka bayar da fitsarinsu domin ta gudanar da gwaji a kansu lokacin gasar kwallon zari-ruga ta duniya.