Rooney zai farfado da mu, in ji Ferguson

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce yana fatan haskakawar da Rooney ya fara yi za ta sa kulab din ya samu tagomashi a gasar Premier League.

Rooney ya zura kwallaye biyu a raga-karo na farko da ya zura kallo a gasar Premier tun watan Satumba- lokacin da suka yi galaba a kan Wolves; suna da ci hudu, Wolves kuma na da daya.

Ferguson ya ce: '' Muna sa ran Rooney zai zura kwallaye da dama, wadanda za su sanya mu samu tagomashi a badi.A koda yaushe ina cewa watan Disamba na da muhimmanci.Idan muka shiga sabuwar shekara a yanayin da muke ciki, muna da dama sosai"

Wadannan kalamai na Ferguson na zuwa ne bayan an fitar da Manchester United daga Champions League da kuma Carling Cup.

Sai dai United na da wasanni hudu a watan Disamba inda zata fafata da kungiyoyin da ke kasan tebur.

Kungiyoyin da ke kasan tebur din kuma za su so matsawa kusa da manyan kulab-kulab.