Arsenal za ta ziyarci Najeriya

Arsenal
Bayanan hoto,

Arsenal dai na da magoya baya sosai a Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila za ta ziyarci Najeriya a badi domin karawa da wasu daga cikin kungiyoyin da ke wasa a rukunin Premier ta Najeriyar.

Daraktan kasuwanci na kungiyar Angus Kinnear ne ya bayyana haka da ya jagoranci tawagar jami'an Arsenal din zuwa ofishin hukumar kwallon kafa ta kasa, NFF a Abuja.

Sakataren riko na Hukumar ta NFF, Barrister Musa Amadu ya shaida wa jami'an na Arsenal cewa 'yan Najeriya na matukar sha'awar kwallon kafa.

"Kasar da ta ke da mutane miliyan 167, wadanda kan taru wuri guda duk lokacin da ake maganar kwallon kafa."

Ya ce shekaru biyu da suka gabata lokacin da Manchester United da Portsmouth suka ziyarci Najeriya sun yi mamakin irin tarbar da masoya kwallon kafa suka yi musu a Najeriya.

Kinnear ya bayyana cewa banda Ingila, babu inda Arsenal ke da yawan magoya baya kamar Najeriya - batun da Amadu shi ma ya amince da shi.

"Mun yi mamakin irin abinda muka gani a nan. Kulob din mu na da 'yan wasa daga kasashe kusan 20, kuma kocinmu na baiwa kwarewa fifiko. Mun fi baiwa horaswa muhimmanci maimakon siyo kwararrun 'yan wasa", a cewar Kinnear.