Man City ta yi watsi da tayin Milan kan Tevez

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni dai dangantaka ta riga ta yi tsami tsakanin Tevez da City

Manchester City ta yi watsi da tayin da AC Milan ta yi na karbar Carlos Tevez a matsayin aro tare da sayensa na din-din-din a kakar badi.

Zakarun gasar Italiya Milan sun mika bukatarsu ga City a ranar 6 ga watan Disamba sai dai City ta shaida wa BBC cewa ta yi watsi da tayin.

Man City na bukatar sayar da dan wasan ne mai shekaru 27 gaba daya ba wai ta bayar da shi aro ba.

Duka Tevez da City sun nanata cewa rahotannin da ke cewa an cimma matsaya da Paris Saint-Germain kan sayen dan wasan ba gaskiya ba ne.

Wata majiya ta kusa da Tevez ta shaida wa BBC cewa: "Babu wata ganawa tsakanin Tevez da PSG.

"Carlos bai yi wata ganawa ba, kuma ba shi da masaniya kan wata jarjejeniya."

Ana ganin dai Milan ce kan gaba wajen yunkurin sayen Tevez, amma har yanzu babu wata matsaya da aka cimma.

Karin bayani