Eto'o ya gurfana gaban kwamitin da'a a Kamaru

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o shi ne kyaftin din Kamaru

Kyaftin din tawagar kwallon Kamaru Samuel Eto'o da jami'an hukumar kwallon kasar sun gurfana a gaban kwamitin da'a bisa zargin yajin aikin bugawa kasar kwallo.

Wannan dai ya biyo bayan yajin aikin 'yan wasa ne wanda ya kai ga soke wasan sada zumuntar da kasar za ta yi da Algeria a watan da ya gabata.

A watan da ya gabata ne aka shirya zaman jin ba'asin amma sai aka dage saboda uzurin 'yan wasan a kulob dinsu.

Eto'o da Eyong wanda shi ne mataimakinsa su ne kyaftin da mataimakin kyaftin, kuma suna cikin 'yan tawagar da suka ki taka ledar sakamakon takaddama kan kudi.

Kamaru ta buga wasannin sada zumunta biyu a Morocco amma basu tafi Algeria ba domin buga na ukun saboda takaddama kan kudi.

Matakin ya haifar da mummunan abin kunya ga Hukumar kwallon kafa ta Kamaru Fecafoot da kuma gwamnati.

A ranar Talata ne ake sa ran kammala sauraran ba'asin amma babu tabbas idan za a bayyana sakamakon nan take.

Dan wasan baya Benoit Assou-Ekotou, shi ma na fuskantar tuhuma, bayan da yaki halartar wasannin gaba daya - ciki harda wadanda tawagar ta buga.

Karin bayani