Andre Santos zai yi jinyar watanni uku

Andre Santos
Image caption Andre Santos yana taka rawa sosai a Arsenal

Dan wasan Arsenal Andre Santos zai yi jinyar watanni uku bayan da ya samu rauni a idan sawunsa a wasan da suka fafata da Olympiakos.

Dan wasan mai shekaru 28 ya bukaci aiki a kafarsa a wasan da Olympiakos ta doke su da ci 3-1 a gasar zakarun Turai.

Gunners ta tabbatar cewa Santos ya samu matsala a idan sahun kafarsa ta dama, wacce aka gyara a Brazil a wannan makon.

Carl Jenkinson da Kieran Gibbs da Bacary Sagna duka suna fama da rauni.

Gibbs ya fara murmurewa daga tiyatar da aka yi masa, kuma ba a sa ran zai dawo sai nan da makonni biyu.

Sagna kuma ya karya kafarsa ne a wasan da Tottenham ta doke su a watan Oktoba.

Karin bayani