Ba za mu nemi Cahill da Modric ba - Villas-Boas

 Andre Villas-Boas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andre Villas-Boas ya fuskanci matsaloli a 'yan kwanakin baya

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce ba zai nemi sayen Gary Cahill ko Luka Modric a watan Janairu ba, lokacin da za a bude kasuwar sayen 'yan wasa.

Za a sake bude kasuwar hada-hadar 'yan wasa nan da makonni uku, amma kocin na Chelsea ya nuna gamsuwa da tawagarsa duk kuwa da cewa ana alakanta shi da yunkurin sayen wasu 'yan wasa da dama.

Daya daga cikin 'yan wasan da ake alakanta wa da Chelsea shi ne dan wasan Ingila Cahill wanda kwantiraginsa da Bolton za ta kare a kakar badi.

"Dan wasa ne mai kyau, saboda yana taka wa tawagar Ingila leda. Dan baya ne kwararre," a cewar Villas-Boas.

"Ya taka rawa sosai a kakar bara duka a Ingila da kuma kulob dinsa. Amma ba ya cikin 'yan wasan da muke son saye."

Wani dan wasan kuma da kocin ya ce ba zai dauka ba shi ne na Tottenham Luka Modric, wanda aka yi ta cece-kuce a kansa a karshen kakar bara.

"Muna da (Michael) Essien wanda zai dawo daga jinya don haka ina ganin mun gama da wannan bangaren," a cewarsa.

Ana kuma alakanta Chelsea da dan wasan Porto Alvaro Pereira, wanda Villas-Boas ya yi aiki tare da shi a Porto.

Karin bayani