Fletcher ya tafi hutu saboda rashin lafiya

Darren Fletcher Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Darren Fletcher ya dade yana taka leda a Man United

Dan wasan Manchester United da kuma Chelsea Darren Fletcher, ya bayyana cewa zai dauki hutu mai tsayi daga fagen kwallon kafa saboda dalilai na rashin lafiya.

Fletcher bai samu damar taka leda a mafi yawancin wasannin kakar da ta gabata ba saboda rashin lafiya.

Sai dai yanzu ya amince da shawarar likitoci na daukar hutu domin ya samu cikakkiyar lafiya.

Darren Fletcher wanda yana taka rawa sosai a Manchester United da kuma Scotland - wannan matakin ba karamin koma-baya ba ne a gareshi da kuma musamman kasarsa ta Scotland.

Karin bayani