Chinedu Obasi na son barin Hoffenhiem

Chinedu Obasi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chinedu Obasi ya yi fama da rauni a kakar wasanni ta bana

Dan wasan Najeriya Chinedu Obasi ya ce yana son barin kulob din Hoffenhiem na kasar Jamus bayan da ya shafe shekaru hudu yana taka leda a can.

Rahotanni sun nuna cewa Schalke na zawarcin dan wasan domin maye gurbin dan kasar Peru Jefferson Farfan, wanda ya samu mummunan rauni a gwiwarsa a watan da ya gabata.

Obasi, mai shekaru 25, yana da kwantiragi da Hoffenheim har zuwa shekaru 2014.

Amma sakamakon raunin da ya yi fama da shi a kakar bana, Hoffenheim ba sa amfani da shi akai-akai yayin da Ryan Babbel ya buga dukkan wasanni 16 da aka fafata kawo yanzu.

"Ina son Hoffenheim, sun bani dama sosai, amma ina ganin lokaci ya yi da za a samu sauyi," kamar yadda ya sahida wa Obasi Bild.

Farfan ya samu rauni ne a gwiwarsa a watan Nuwamba lokacin da yake takawa Peru leda, kuma ana sa ran ba zai dawo ba har sai watan Janairu.

Karin bayani