ACN: Yaya Toure ya nuna damuwa

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yaya Toure yana taka rawa sosai a Ivory Coast da Man City

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ya nuna "damuwa" kan barin kulob dinsa domin halattar gasar cin kofin kasashen Afrika a watan gobe.

Ivory Coast na bukatar Toure domin halattar gasar wacce za a yi a kasashen Gabon da Equatorial Guinea daga ranar 21 ga watan Janairu.

"Kasa ta na bukatar mutane kamar ni da Drogba a wannan gasar," a cewar Toure.

"An yi yaki a kasar, don haka yana da muhimmanci mu yi abinda ya kamata ga kasarmu domin mutane suna cikin tsoro.

"Kulob di na da sauran abokan wasa na suna bukata ta, don haka ina cikin rudani da rashin kwanciyar hankali kan tafiyar tawa."

Shekara guda bayan yakin basasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar a bara - yakin da ya jefa tsoro cikin zukatan 'yan kasar.

Karin bayani