Ayew ya sabunta kwantaraginsa da Marseille

Andre Dede Ayew
Image caption Andre Dede Ayew

Dan wasan Ghana da kuma kungiyar kwallon kafa ta Marseille wato Andre "Dede" Ayew wanda ya ci gwarzon dan wasan BBC na bana, ya sake sanya hannu a sabon kwantaragi da klub din sa, wanda ba zai kare ba sai shekarar 2015.

Sanarwar ta samu ne a shafin internet na klub din na kasar Faransa a ranar Lahadi, bayanda aka bada sanarwar cewa shi ne gwarzon dan wasan Africa na BBC a bana.

Dan wasan na tsakiya mai shekaru 21 a duniya, ya samu lambar kyautar ce a ranar Jumuar da ta gabata, kuma ya daga kyautar a gaban magoya bayan klub din a ranar Asabar.

Mai horar da yan wasan Marseille Didier Deschamps ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafar za ta dogara ne gare shi a badi.

Ayew dai, wanda 'da ne ga tsohon shahararren dan wasan na Marseille Abedi Pele, ya samu horo ne a makarantar koyon kwallon kafa ta klub din na Marseille, kuma shi ne zakaran klub din na shekarun 2010 zuwa 2011.