Wasa a gida ya bamu dama, in ji Mancini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce kulab dinsa na da babbar dama ta lashe gasar Premier ta Ingila saboda sun kawar da abokan hamayyarsu na kur-kusa.

City dai ta ci wasanninta guda takwas da ta buga a filin wasa na Etihad.

Mancini ya ce: "mun gwabza da Tottenham inda su suka same mu a gidanmu, kana mun doke United, da Chelsea da kuma Liverpool a waje.Buga wasa a gida na da wuya, sai dai hakan dama ce a gare mu''.

Manchester City ta ci kwallaye ashirin da biyar a wasanni takwas da ta buga na gasar Premier a filin wasan Etihad.

Mancini ya ce:" A watanni biyu masu zuwa, United za ta kara da Tottenham, da Chelsea, da kuma and Arsenal a waje.Hakan na da muhimmanci''.