Kwallon kafa na da muhimmanci ga Nigeria, in ji sarkin musulmi

Sarkin musulmi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarkin musulmi

Sarkin musulmi Alh Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa, da su ajiye duk wata adawa, su mara wa kwamitin zartarwar hukumar kwallon kafar kasar NFF karkashin jagorancin Alh Aminu Maigari.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a lokacin da shugaban kwamitin zartarwar hukumar ta NFF Alhaji Aminu Maigari tare da mukarraban sa suka kai masa ziyara.

Sarkin musulmin ya yi kira ga hukumar ta NFF da ta tashi tsaye ta bullo da shirin da zai sake farfado da kwallon kafa a Nigeria cikin shekara mai zuwa.

A cewar sarkin musulmin, kwallon kafa na da matukar muhimmanci ga yan Nigeria, domin ko ba komi ya na taimakawa wurin hada kan yan kasar.