Ana zargin Terry da yin kalaman batanci ga Fadinand

John Terry Hakkin mallakar hoto PA
Image caption John Terry

Masu gabata da kara na Birtaniya sun ce, kyaptin din yan wasan kasar Ingila John Terry zai fuskanci kuliya bisa zargin sa da yin kalaman batanci masu alaka da banbancin launin fata.

Ana zargin Terry ne da yin kalaman a kan Anton Ferdinand, dan wasan Queens Park Rangers, a lokacin wasan da suka buga a watan October, inda Chelsea ta yi nasara da ci daya da nema.

An yi wa kyaptin din na Chelsea tambayoyi a karkashin matakai cikin watan Nuwamba, wanda daga bisani aka aike da takardar bayani ga masu gabatar da kara na Birtaniya a watan December.

Dan shekaru 30 a duniya, ya sha musanta cewa ya yi wasu kalamai na batanci.

John Terry dai zai gurfana a gaban alkali a ranar 1 ga watan Fabrairun badi.