Mai yiwuwa Arsenal ta nemi aron 'yan wasa- Wenger

Hakkin mallakar hoto a
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce watakila ya nemi aron 'yan wasa idan Kieran Gibbs bai dawo kulab din da wuri ba sakamakon jinyar da ya ke yi ta cutar kaba.

Da ma dai masu tsaron gidan kulab din irinsu Bacary Sagna, da Carl Jenkinson, da Andre Santos da kuma Johan Djourou suna can suna murmurewa daga raunukan da suka samu.

Gibbs na dab da dawowa sai dai Wenger ya ce watakila ya nemi aron dan wasan baya saboda babu isassun 'yan wasan baya a kulab din.

Wenger ya ce:''Muna duba yiwuwar samun 'yan wasa idan Gibbs bai dawo ba''.