Ban yi nadamar `kin bugawa Kamaru wasa ba - Eto'o

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto'o

Kaftin din 'yan wasan kwallon Kamaru Samuel Eto'o ya ce bai yi nadamar matakin `kin bugawa kasarsa wasa ba, wanda yayi sanadiyar takunkumin hana shi bugawa Kamaru wasanni goma sha biyar da aka sanya masa.

Hukumar kwallon kafa ta Kamaru ne dai ta sanya takunkumin bayan da 'yan wasan suka `ki zuwa domin buga wasan sada zumunta tsakanin Kamaru da kasar Aljeriya sakamakon ce ce kuce na jinkirin biyansu kudaden alawus alawus.

Samuel Eto'o , ya ce dukkan 'yan wasan basu yi nadamar matakin da suka dauka ba, illa sun yi amfani da damar da suke da ita ce don ganin an magance matsalolin da suka dabaibaye harkar wasan kwallon kafa a Kamaru.

Kaftin din 'yan wasan kasar Kamarun wanda bai kalubalanci matakin takunkumin da aka sanya masa ba, ba zai taka leda ba a dukkan wasannin share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2013 da wasannin shara fagen shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2014 da Kamaru zata buga.

Tun da farko wasu masu sha'awar kwallon kafa a Kamaru sun shirya gudanar da zanga zanga don nuna goyon bayansu ga Samuel Eto'o , sai dai dan wasan ya ce hakan bai da wani muhimmanci, inda ya tabbatar da cewa zai ci gaba da bugawa kasarsa wasa bayan cikar wa'adin takunkumin matukar yana iya taka leda.

Karin bayani