Terry zai doka wasan da chelsea za ta yi a yau

Kyaptin din Chelsea John Terry Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kyaptin din Chelsea John Terry

Dan wasan klub din Chelsea kuma kyaptin din yan wasan Ingila John Terry zai taka leda a wasan da za su buga da Tottenham a yau.

Terry zai buga wasan ne, saoi ashirin da hudu bayan zargin sa da kalaman batanci masu nasaba da banbancin launin fata.

Tuni dai ya musanta yin duk wani ba daidai ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da gaskiyar sa.

Wakilin BBC ya ce a matsayin sa na kyaptin din yan wasan Chelsea, shariar ka iya shafar shirin klub din na fuskantar wasannin zakarun turai.