Mourinho na son komawa Ingila

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto 1

Tsohon kocin kulob din Chelsea Jose Mourinho ya ce mataki na gaba da zai dauka a horar da 'yan wasa shi ne ya koma gasar Pirimiya.

Mai horar da 'yan wasan dan kasar portugal wanda a yanzu shi yake horar da 'yan wasan kulob din Real madris a kasar Spain, ya ce duk da cewa yana jin dadin aiki a Real Madrid a yanzu, amma 'sha'awar sa na Ingila'.

A wata hira da BBC, Mourinho ya ce "Mataki na na gaba shi ne in koma Ingila".

Sannan cikin raha ya cewa mai gabatar da shirin ya samar masa kulob din da zai horar a cikin shekaru masu zuwa.

Mourinho ya bar Chelsea ne a shekarar 2007 bayan ya lashe gasar Pirimiyar Ingila biyu, da kofin FA da na League. Ya kuma lashe gasar zakarun turai har sau uku, da kofin League din Italiya da kulob din Inter Milan, sannan ya koma kulob din Madrid a shekarar 2010.

An dai jima ana alakanta shi da komawa kulob din Mancheter United domin ya gaji Sir Alex Ferguson idan ya yi ritaya.

Karin bayani