Paulo ne sabon kocin Equatorial Guinea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon kocin Equatorial Guniea Henri Michel ya ajiye aikinsa ne a watan daya gabata.

Equatorial Guinea ta bayyana dan Brazil Gilson Paulo a matsayin kocinta a yayinda ake makwanni biyu kafin a fara gasar cin kofin Afrika da kasar da kuma Gabon za su karbi bakunci.

Kocin mai shekarun haihuwa 62, zai maye gurbin dan Faransa Henri Michel, wanda ya ajiye aikinsa a watan da ya gabata.

Kocin zai jagoranci kasar a karon farko a wasan sada zumunci da tawagar kasar za ta buga da kasar Afrika ta kudu.

Michel dai ya ajiye aikinsa ne saboda adawa da tsoma bakin da Ministan wasanni yake yi a harkar kwallon kafan kasar.

Equatorial Guinea, dai za ta buga gasar cin kofin Afrika ne a karo ne farko, kuma za ta buga a rukunin A ne da kasashen Zambia da Senegal da kuma Libya.