Roberto Mancini ya jinjinawa Yaya Toure

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaya Toure

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce ba za a iya maye gurbin Yaya Toure a tawagar Manchester City ba.

Toure ne ya zura kwallo ta biyu da City ta ci a nasarar da kungiyar ta yi akan Liverpool da kwallaye uku da nema a filin Etihad.

Dan wasan dai na shirin komawa tawagar Ivory Coast ne a shirye shiryen da kasar ke yi na halartar gasar gasar cin kofin Afrika.

Yaya Toure dai zai takawa City leda a wasan da za ta buga da United a gasar cin kofin FA a ranar Lahadi kafin ya koma kasarsa.

"Na yi kokarin samu wani Yaya a tawaga ta amma babu wani." In ji Mancini.

"Yana da mahimmaci, saboda haka akwai kalubale a gabanmu a wannan watan.

"Idan har zamu iya zama a saman tebur har karshen watan Junairu, ina da kwarin gwiwa zamu lashe gasar ta Premier."