Kolo da Yaya Toure ba za su takawa City leda a kofin FA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kolo Toure

Kocin Ivory Coast Francois Zahoui ya yi watsi da bukatar Manchester City na neman Yaya da Kolo Toure su takawa Manchester City leda a wasan da za ta buga da United a gasar cin kofin FA.

"Kungiyoyi sun san dokokin," In ji Zahoui. "Ina sauraren 'yan wasan biyu kafin wa'adin da Fifa ta bada ya cika."

Karkasin dokokin Fifa, za a iya kira 'yan wasa daga kungiyoyinsu makwanni biyu kafin a fara gasar cin kofin Afrika wanda za'a fara a ranar 21 ga watan Junairu.

City dai na fatan 'yan wasan biyu za su taka mata leda a wasanta da United, kafin su wuce sansanin horon Ivory Coast a shirye shiryensu na halartar gasar cin kofin Afrika.

Amma Zahoui ya nace cewa sai 'yan wasan sun gana da shi a birnin Paris a ranar asabar sannan su tashi da sauran tawagar kasar zuwa Abu Dhabi, inda za su yi horo na makwanni biyu.