Manchester United ba ta cikin fargaba- Ferguson

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kocin United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya nace cewa kungiyar ba ta cikin fargaba duk da kashin da ta sha a hannun Newcastle United.

Newcastle dai ta lallasa Manchester United ne da ci uku da nema.

Rashin nasarar da United ta samu shine na biyu cikin kwanaki biyar.

"Mu na da kwarewar da zai taimaka mana.. ya kamata kuma mu rika nuna hakan indan munyi tattaki.

A yanzu haka dai United ce ta biyu a tebur, kuma tana bayan City ce da maki uku.