Henry ya koma Arsenal na watanni biyu

henry Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thierry Henry

Thierry Henry ya koma Arsenal a matsayin aro na watanni biyu daga kungiyar New York Red Bulls.

Tsohon kyaftin din Arsenal din mai shekaru 34 yana horo da kulob din lokacin hutun da ake yi hutu a gasar kwallon Amurka.

Dan wasan zai buga wasanni tare da kulob din a watan Junairu da Fabarairu a yayinda Gervinho ya tafi kasarsa don buga gasar kwallon kasashen Afrika.

Henry zai iya buga wasan Arsenal da Leeds na gasar kofin FA, kuma kocinsa Arsene Wenger ya ce "na ji dadi kuma burina ne kamar yadda shima Thierry yake so".

Ya kara da cewar " Zamu samu Thierry a watan Junairu da Fabrairu kafin ya koma Amurka".

Karin bayani